fbpx
Saturday, April 17
Shadow

Rundunar tsaro ta Amotekun ta kubutar da mutane 3 da aka sace a Jihar Ondo

Rundunar Amotekun sun ceto mata biyu da wani namiji daga hannun ’yan bindiga suka sace lokacin da suke tafiya daga Jihar Benuwai zuwa Akure bayan hidimar coci.

An bayar da sunayen wadanda abin ya shafa kamar haka; Mista Adewale Adebisi mai shekaru 52; Miss Ahan Mary 21 da Miss Ladi Bude 23.

An sace su ne a ranar Asabar tare da hanyar Ifira – Iduani a karamar hukumar Ose.

An kuma kame mutane 2 da ake zargi da hannu wajen garkuwa da mutanen.

An bayyana cewa, rundunar Amotekun ta samu kiran gaggawa inda suka hanzarta zuwa dajin.

Direban motar bas din, Adebisi ya ce sun dawo ne daga harkokin coci sai samari takwas da suka fito daga daji suka tare masu hanya.

Kwamandan Ondo Amotekun, Cif Adetunji Adeleye, ya tabbatar da kubutar da mutanen uku.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *