fbpx
Sunday, September 26
Shadow

Rundunar ‘yan sanda a jihar Taraba ta tabbatar da kisan wasu makiyaya 6

Kakakin rundunar ‘yan sandan Taraba, ASP Abdullahi Usman, ya shaida wa manema labarai cewa an kashe samari hudu da mata biyu a wani harin ramuwar gayya.

Ya ce an kashe su ne a wani hari da aka kai a kauyen Mungadoso da ke karamar hukumar Karim-Lamido na jihar ranar Litinin.

ASP Abdullahi Usman ya bayyana cewa wasu mutane sun kai hari kan wata rugar Fulani a yankin lokacin da suka tsinci gawar wani mutum da ya bata a kauyen kwanaki biyu kafin faruwar lamarin.

Ya ce mutanen garin sun dora alhakin mutuwar mutumin a kan makiyaya, wanda ya kai ga daukar fansa.

Ya ce wasu mutane hudu da ke zaune a yankin sun bata kuma ’yan sanda da’ yan banga suna cikin daji suna neman mutanen da suka rasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *