fbpx
Thursday, July 29
Shadow

Rundunar Yan sanda ta cafke mutane 1,320 da ake zargi da aikata laifuka, tare da kwato makamai 110 a Legas

Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta ce ta cafke mutane wadanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban su 1,320 kuma ta kwato makamai 110 tsakanin 1 ga Mayu zuwa 13 ga Yuli.

Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Legas, CP Hakeem Odumosu, ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a Legas ranar Laraba.

Odumosu ya ce an kwato harsasai guda 125 da motoci takwas da aka sace.

Odumosu, wanda ya danganta kamun da kafa wasu rundunoni na baya-bayan nan, ya kara da cewa rundunar ta kuma iya dakile kararraki 46 na fashi da makami a cikin wannan lokaci.

Ina so in sake jaddada aniyarmu da jajircewarmu na yin amfani da duk wata hanya ta rage aikata laifuka da munanan halaye a cikin Legas, ”inji shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *