fbpx
Monday, October 25
Shadow

Rundunar yan sanda ta cafke mutane 259 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar Neja

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta cafke kimanin mutane 259 da ake zargi da laifin fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran laifuka a watan Agusta.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Monday Kuryas, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya a Minna ranar Asabar cewa an aka aikatan laifuka a kananan hukumomi 25 na jihar.

“Mun gurfanar da mutane 119 cikin 259 da aka kama a kotu, 81 daga cikinsu har yanzu suna nan a gaban shari’a,” in ji shi.

Ya kara da cewa mutane 59 da ake tuhuma har yanzu ana binciken su a ofishin binciken manyan laifuka na jihar, yayin da aka aika da kararraki tara zuwa ma’aikatar shari’ar jihar don tantancewa da shawarwarin shari’a.

Ya bayyana cewa rundunar ta kuma kwato bindigogi guda uku da aka kera a cikin gida, bindigar Dane guda daya, da bindigogi biyu da aka kera a cikin gida tare da harsasai guda uku.

Kwamishinan ‘yan sandan ya kuma shaida wa NAN cewa, rundunar ta magance matsalar‘ yan fashi a kauyen Ma’undu da ke karamar Hukumar Mariga, wanda ya kasance sansanin ‘yan ta’adda.

“Muna rokon tallafi da hadin kai daga jama’a wanda yakamata ya bamu bayanan sirri da zasu taimaka wajen kama masu bata gari a tsakanin su.

“A shirye muke mu tunkari duk wani mutum ko gungun barayi masu lalata yanayin zaman lafiya da aka san jihar mu da shi ta hanyar ingantattun hanyoyin tsaro don haɓaka zaman lafiya tsakanin mutanen mu,” in ji Kuryas.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *