fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Rundunar yan sanda ta kama masu garkuwa da mutane 4 a jihar Kogi

Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta ce ta cafke mutane hudu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne da‘ yan fashi da makami da ke addabar mazauna karamar hukumar Bassa da kewayenta.

Sanarwar da mai magana da yawun rundunar, DSP William Ayah ya fitar, ta ce an gano makamai da alburusai daga wadanda ake zargi, wadanda suka hada da bindiga kirar gida guda daya, alburusai 7.62mm, harsashi daya, harsasai G3 guda daya da kuma kan mutum guda biyu.

“Bayan bayanan sirri masu sahihanci sun gano wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane da fashi da makami da ke addabar karamar hukumar Bassa da kewayenta a cikin wani fili, sabon yankin Jerusalem Oguma a Bassa, Jami’an rundunar‘ yan sandan Najeriya da ke aiki a sashin Bassa da DPO ke jagorantarta suka shiga aiki cikin gaggawa. ”

“Sun kutsa cikin harabar kuma suka cafke wadanda ake zargi; Guda Dangana, Dogo Chure, Dekina Zhiya, Samson Nyizo, duk daga Karamar Hukumar Bassa. ” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ci gaba da jaddada cewa wadanda ake zargin sun yi ikirari mai amfani kan jerin laifuka a cikin yankin Bassa kuma za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.

“Kwamishinan‘ yan sandan, CP Idrisu Dauda Dabban, yayin da yake yabawa jami’an da suka gaggauta mayar da martani, ya tabbatar wa da jama’a cewa rundunar ‘yan sandan jihar Kogi tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro a jihar ba za su yi kasa a gwiwa ba kan kama masu aikata laifuka a cikin jihar, ”in ji shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *