fbpx
Thursday, April 22
Shadow

Rundunar Yan Sanda Ta Karrama Sarkin Bauchi Domin Kawo zaman Lafiya a Jiharsa

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Bauchi ta ba da lambar girma ga mai martaba Sarkin Bauchi, Dr Rilwamu Suleiman Adamu, saboda inganta zaman lafiya a yankinsa da jihar.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Bauchi, Sylvester Abiodun Alabi, wanda ya gabatar da kyautar ga sarkin a fadarsa, ya bayyana masarautar a matsayin wani abu mai hada kai wanda ya nuna jajircewa wajen tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a Bauchi.
Kwamishinan ya tabbatar wa Sarkin cewa rundunar za ta ci gaba da cika ayyukanta ta hanyar kiyaye dorewar lafiyar jama’a, tsaro da kuma bin doka da oda.
Ya yi kira ga mazauna jihar su yi koyi da basaraken kuma su ci gaba da aiki tare da ‘yan sanda ta hanyar kai rahoton duk wani motsin da ba su yarda da shi ba ga rundunar da nufin tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Da yake mayar da martani, Mai martaba Sarkin Bauchi, Dokta Rilwan Sulaiman Adamu ya bukaci sabon kwamishinan ‘yan sanda da nuna adalci a yayin sauke nauyin da aka dora masa.
Ya kuma bukaci mutanen jihar da su ba jami’an tsaro hadin kai a kokarin su na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *