fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Rundunar ‘yan sandan Kaduna ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da kashe dan Sanata Na-Allah

An cafke mutane biyu da ake zargi da kisan Abdulkarim Na-Allah, babban dan Sanata Bala Ibn Na-Allah da rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta yi.

Sanata Na’Allah yana wakiltar gundumar Kebbi ta Kudu a Majalisar Dokoki ta kasa.

ASP Mohammed Jalige, jami’in hulda da jama’a na rundunar, ya tabbatar da cewa an cafke mutanen biyu da ake zargi mako guda da ya gabata a Kaduna.

A cewarsa, ana ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin kisan dan Sanatan a Kaduna.

Ya kuma tabbatar da cewa an gano motar da wadanda ake zargi suka kwace daga mamacin, ya kara da cewa tana cikin Jamhuriyar Nijar.

Ya yi bayanin cewa rundunar tana hada gwiwa da Interpol don dawo da motar zuwa Najeriya.

Ku tuna cewa a ranar 29 ga Agusta, 2021, ‘yan sanda sun tabbatar da kisan Abdulkarim Na-Allah lokacin da aka tsinci gawarsa a dakinsa da ke Malali GRA, Kaduna.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *