fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Rundunar ‘yan sandan Najeriya na cikin shirin ko-ta-kwana kan kisan Soleimani

Rundunar sojin Najeriya ta baza ‘yan sanda a fadin kasar bayan da Amurka ta kashe kwamandan sojin kasar Iran, Qasem Soleimani.

A ranar Juma’a ne dai wani jirgin Amurka maras matuki ya hallaka Soleimani tare da wasu sojojin sa-kai na Iraqi a Baghdad.
A ranar Lahadi ne dai rundunar ‘yan sandan ta wallafa sanarwa a shafinta na Twitter cewa sifeto janar na kasar ya umarci ‘yan sandan kasar su kasance cikin ko-ta-kwana.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Rundunar dai ba ta bayar da wani dalilin daukar wannan mataki ba sai dai ana ganin hakan ba ya rasa nasaba da irin alakar da ke akwai tsakanin mabiya kungiyar Islamic Movement of Nigeria ta Sheikh Zakzaky da kasar Iran.

Ko a ranar Juma’ar da abin ya faru sai da ‘yan kungiyar suka fitar da wata sanarwar Alla-wadai da kisan da Amurkar ta yi wa Qasem Soleimani, al’amarin da ke nuni da cewa ‘yan kungiyar ka iya yin jerin gwanon nuna kyamar al’amarin a Najeriya.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *