fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Ruwan Sama Tare Da Iska Mai Karfi Sunyi Sanadiyyar Rushewar Gidaje 200 a Jihar Taraba

Wata mahaukaciyar guguwa tare da ruwa mai karfi ya lalata gidaje sama da 200 da dukiyoyi na miliyoyin nairori a garuruwan Wukari da Donga da ke Taraba a ranar Laraba.

Mazauna garuruwan biyu, Idi Muhammed da John Dauda sun shaida wa Aminiya a tattaunawarsu daban-daban cewa guguwar ta biyo bayan ruwan sama mai karfi wanda ya kwashe kimanin awanni biyu.
Idi Muhammed ya ce gidaje da yawa, coci da ababen hawa da guguwar ta lalata Wukari.
Ya ce sakamakon haka, mutane da yawa sun rasa gidajen su.
Ba a samu rahoton asarar rai ba.
John Dauda ya kuma shaida cewa gidaje da yawa sun rushe sakamakon guguwar iska a garin Donga a daren Laraba.
Ya ce mazauna da suka rasa gidajensu na zaune a gidajen dangin da guguwar ba ta shafi gidajensu ba.
Wadanda abin ya shafa sun yi kira ga jihar Taraba da ta taimaka musu da rufin kwano domin gyara gidajensu.
Shugaban karamar hukumar wukari na yankin, Adi Daniel Grace ya yi kira ga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta jihar da ta kawo dauki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *