fbpx
Wednesday, January 26
Shadow

Saboda bukukuwan karshen shekara dana Kirsimeti>>Gwamnatin tarayya tace a hau jirgin kasa kyauta

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, a hau jirgin kasa kyauta daga ranar Juma’a har zuwa ranar 4 ga watan Janairu.

 

Gwamnatin tace ta dauki wannan mataki ne dan saukakawa ‘yan Najeriya yawan tafiye-tafiye da ake a karshen shekara.

 

Fidet Okhiria, shugaban hukumar kula da sufurin jirgin kasa na Najeriya ne ya bayyana haka.

 

Ya bayyana cewa, za’a karbi tikitin shiga jirgin amma babu maganar biyan kudi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *