fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Saboda San da nakewa Hrithik Roshan har mafarkinsa nake>>Rahama Sadau

Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta bayyana itin soyayyar da takewa taurarron fina-finan Kasar India, Hrithik Roshan da cewa har mafarkinshi take.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Rahama ta bayyana hakane a cikin wata tambaya da amsa data baiwa masoyanta damar mata, musamman akan sabon fim dinta na Mati A Zazzau.

An tambayeta ne akan shin tsakanin Hrithik Roshan da Priyanka Chopra wata fi so? Sai ta bada amsar cewa, tab ai ta fi son Hrithik Roshan dan shi har mafarkinshi take.

Wasu karin tambayoyi da ta amsa sun hada da cewa Ali Nuhu, Yaseen Auwal da Falalu A. Dorayine gwanayen masu bada umarninta.

Sannan An tambaye ta tsakanin Sadiq Sani Sadiq da Adam A. Zango wa ta fi so? Ta bayyana cewa Sadiq ne a farko sannan sai Adam A. Zango.

An tambayeta kudin da ta kashe wajan shirya fim din Mati a Zazzau amma tace ba zata fada ba sai bayan fim din ya fito.

Rahama Sadau ta bayyana cewa tana da Saura yi kuma a lokacin da ake mata tambayayoyin yana nan yana bibiyarta.

Am kuma Tambayi Rahama cewa shin tana da shirin fitowa a fina-finan kasar Amurka nan gaba inda ta bayar da Amsar cewa Eh.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *