Tauraron fina-finan Hausa, Sadiq Sani Sadiq na murnar cika shekaru 8 da yin aure.
Sadiq ya saka hotunansa da iyalinsa a shafinsa na sada zumunta inda yayi godiya ga Allah da kaiwa wannan matsayi.
Yace matarsa bata taba yi masa abinda yasa yayi dana sanin aurenta ba, dan hakane ma yake godewa Allah da cewa yayi dacen Mata.