fbpx
Sunday, September 26
Shadow

Sai an biyamu Miliyan 81 kamin mu sako daliban Kaduna>>’Yan Bindiga

‘Yan Bindigar da suka sace daliban makarantar Bethel Baptist dake Maraban Rido a Kaduna,  sun bayyana cewa ba zasu sako sauran daliban ba sai an biyasu kudin fansar Miliyan 81.

 

A baya dai ‘yan Bindigar sun sako wasu daga cikin daliban wanda Rahotanni suka bayyana cewa an biya 500,000 kan kowane dalibi.

 

Amma a yanzu, daya daga cikin fastocin dake shiga tsakani kan tattaunawa da ‘yan Bindigar ya bayyana cewa ‘yan Bindigar na neman Miliyan 1 akan kowane dalibi dake hannunsu.

 

A jiya dai muka ji cewa an gano 3 daga cikin daliban wanda ‘yan Bindigar suka barsu a daji.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *