fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Samari 17 sun mutu a wani mummunan hatsarin mota a kan babbar hanyar Zaria zuwa Kano

Akalla samari 17 da suka dawo daga bikin aure a ranar Asabar sun halaka a wani mummunan hatsarin mota a kan hanyar Zaria zuwa Kano.

Rahotannin sun nuna cewa mamatan sun je Zaria ne don halartar bikin auren wani abokinsu.

Rahoton ya tabbatar da cewa 11 daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su sun mutu nan take yayin da wasu shida kuma suka mutu a asibitin da ake kula da su.

Ba zato ba tsammani, duk waɗanda hatsarin ya rutsa da su sun fito ne daga Gwale, wata anguwa dake cikin birnin Jihar Kano.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *