fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Sanata Abaribe yace zai sake tsayawa Nnamdi Kanu a Shari’ar da ake masa

Sanata Enyinnaya Abaribe ya bayyana cewa idan za’a sake bayar da belin Nnamdi Kanu, zai iya sake tsaya masa a bashi belinsa.

 

Abaribe ya bayyana hakane a ganwar da aka yi dashi a TVC. Ya bayyana cewa, kada a dora masa laifin tserewar Nnamdi Kanu daga Najeriya.

 

Yace a wancan lokacin, da aka ga Kanu a kasar Isra’ila,  ya aikewa da ma’aikatar harkokin kasashen waje ta Najeriya da bukatar bucikawa dan gano cewa idan da gaske Kanu ne amma basu amsashi ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *