fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Sanata Ndume ya nemi daina tsayawa Abdulrashid Maina amma kotu tace ba zata yiyu ba

Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta yi watsi da buƙatar Sanata Ali Ndume ta neman ficewa daga matsayinsa na wanda ya tsaya wa Abdulrasheed Maina a shari’ar cin hanci da rashawa da ake yi masa bayan ya karya ƙa’idojin beli.

Kamfanin labarai na NAN ya ruwaito cewa Mai Shari’a Okon Abang ya kamanta buƙatar da Ndume ya gabatar a matsayin cin mutuncin shari’a saboda ya gabatar da irin wannan buƙatar a gaban Kotun Ɗaukaka Ƙara.

Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban rusasshen kwamatin fansho mai suna Pension Reformed Task Team (PRTT), ya tsallake tare da karya ƙa’idojin beli a watan Satumban 2020 bayan an sake shi daga Gidan Yari na Kuje a Abuja.

Sai dai an sake kama shi a Nijar bayan ya tsere, ind aka sake gurfanar da shi gaban kotun ranar 4 ga Disamban 2020.

Tun farko an saki Maina ne bayan Sanata Ndume mai wakiltar Mazaɓar Borno ta Kudu ya tsaya masa ta hanyar yin amfani da kadarorinsa na Abuja da suka kai darajar naira miliyan 500 a matsayin beli kamar yadda kotu ta sharɗanta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *