Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa Tubabbun Boko Haram na yiwa kungiyar leken Asiri a cikin jama’a sannan kuma su sake komawa cikinta.
Gwamnan ya nemi a rika yankewa ‘yan Boko Haram din hukunci kawai idan an kamasu.
A martaninsa ga wannan lamari, Tsohon sanata me wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa, yana baiwa mutane dalilin da yasa ‘yan Boko Haram da suka tuba ke sake komawa kungiyar shine Jini ya fi ruwa Kauri.
Repentant terrorists become spies because blood is thicker than water.
— Senator Shehu Sani (@ShehuSani) March 5, 2021