fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Sanata Shehu Sani ya bayyana abinda ya kamata ayi kan daliban Kaduna 17 da ‘yan Bindiga suka ce zasu kashe a yau

A jiyane dai ‘yan Bindigar da suka sace daliban jami’ar Greenfield dake jihar Kaduna suka bayyana cewa suna bukatar Miliyan 100 daga Gwamnati da kuma Mashina 10 sabbi zuwa yau, Talata idan ba haka ba, zasu kashe sauran dalibai 17 dake hannunsu.

 

A baya dai ‘yan Bindigar sun kashe 5 daga cikin daliban, kuma iyayen daliban sun aike musu da Naira Miliyan 55 a matsayin Kudin fansa, saidai da yake magana da VOA Hausa, Shugaban ‘yan Bindigar ya bayyana cewa, sun kashe wadancan kudi wajan ciyar da daliban.

 

Wannan lamari ya tayarwa da ba iyayen yaran kadai ba ko gwamnatin jihar Kaduna ba hankali, harma da sauran duka ‘yan Najeriya inda ake ta bayar da shawarwari kan matakan da ya kamata a dauka.

 

Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa, bai kamata a cutar da sauran dalibai 17 da suka rage na jami’ar Greenfield ba. Yace idan gwamnatocin jihohi dana tarayya suka zabi kin yin komai akai, babu abin da zai hana ‘yan majalisar jihar da sauran masu mukamai a gwamnatin tarayya daukar mataki. Yace abin yana bukatar agajin gaggawa.

The Remaining 17 Greenfield Students must not be harmed.If the State & Federal Government has chosen to do nothing about it,nothing stops the Federal & State Lawmakers & Federal Appointees from the state from reaching out to the Parents of the abductees.This is an emergency.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *