fbpx
Monday, May 10
Shadow

Sanya dokar Ta-baci ba za ta magance rashin tsaro ba>>Masari

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya shawarci cewa sanya dokar ta baci ba zai magance kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta ba.
Masari ya ba da shawarar ne a ranar Alhamis yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai na fadar gwamnati bayan ganawa da Shugaban Ma’aikata na shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, a Fadar Shugaban Kasa, Abuja.
Idan za a iya tunawa, majalisar wakilai a ranar Talata ta nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya gaggauta sanya dokar ta-baci a bangaren tsaro don magance matsalar rashin tsaro a kasar nan.
A cewarsa, sojojin da za a yi amfani da su don aiwatar da irin wannan yanayin na gaggawa an riga an yi amfani da su.
Don haka gwamnan ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su daina sanya siyasa a cikin al’amuran tsaro, yana mai cewa ayyukan yan sanda a kasar a wannan mawuyacin lokaci ya zama aikin kowa.
Ya ce ba za a bar Najeriya ta wargaje ba domin hakan na nufin babbar matsala ga nahiyar Afirka baki daya.
Masari, yayin da yake magana a kan fargabar cewa Kwamitin Raba Asusun Tarayya (FAAC) ba zai iya rarraba kason kudin na wata-wata na watan Mayu ba, ya kalubalanci hukumomin da abin ya shafa don tabbatar da hanyar da za ta kau da hakan.
Ya ce rashin iyawar jihohi da kananan hukumomi na daukar nauyin ayyukansu na iya kara tabarbarewar matsalar tsaro a kasar nan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *