fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Sanyi ya daskarar da Jaririn da iyayensa suka barshi a waje

Masu gudanar da bincike a kasar Rasha sun kafa wani kwamitin bincike na tuhuma bayan da wasu iyaye suka bar jariri a baranda sanyi ya kashe shi inji jami’ai.

Jaririn dan wata bakwai da haihuwa wanda aka saka shi a cikin keken tura jarirai, an bar shi ne cikin matsanancin sanyi har na tsawon sa’a biyar a yankin gabashin Khabarovsk.
An ajiye shi ne a barandar yana barci domin samun wadatacciyar iska, kamar yadda kafafen yada labarai na yankin suka rawaito.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Daga baya dai ma’aikatar lafiya ta yankin ta bayar da shawarar a daina barin yara a waje ba tare da kulawa da su ba.

“A ko da yaushe, ku dinga sanin inda yaranku suke kuma a wajen wa suke,” in ji hukumar a wani sako da ta wallafa a shafin Instagram.

Ta kuma kara da cewa, idan kuka ga yaro cikin hadari to kada ku wuce – a lokacin sanyi, yaron da ya bata ko kuma ya sami rauni a titi na da saurin kamuwa da sanyi.

Hukumar ta kuma ce ana kara samun yaran yankin Khabarovsk da ke cikin yaran da ke fama da rashin kulawa na iyaye da nuna halin ko-in-kula da ta kwatanta a matsayin matakan farko da ya kamata a dauka don kulawa.

A cewar wani shafin labarai na Rasha mai suna Lenta, wani rahoto da aka kaddamar a kan mutuwar yaron a birnin Nikolayevsk-on-Amurya ya nuna cewar yaron ya mutu ne sakamakon “hypothermia”.

Matsalar Hypothermia ta kan faru ne idan jikin mutum ya kasance babu zafi ko dumi sakamakon barin shi cikin tsananin sanyi.

Ya kan iya faruwa ma a lokacin da ba na sanyi ba idan har mutum ya dade cikin sanyin.

Mutane masu yawan shekaru da kuma yara ‘yan shekara daya sun fi shiga hadarin kamuwa da wannan cuta cikin sauran mutanen da ba su da wata matsalar lafiyar jiki.

Kai yara kanana waje domin su yi barci ba wani bakon abu ba ne a kasashen da ke da yanayi na sanyi sosai.

Manufar kai yaran waje domin samun iska sosai su yi barci ko a lokacin sanyi shi ne zai iya taimakawa wajen kare su daga kamuwa da tari da kuma cutukan da sanyi ke haddasawa.

Iyaye da ke arewacin kasashen Turai irin su Finland da Norway su ma sun yi imanin cewa yaransu sun fi samun barci yadda ya kamata da kuma dogon barci idan su ka bar su a waje.
BBChausa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *