fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Sarauniya Elizabeth ta kwana a asibiti

Fadar Buckingham ta ce Sarauniya Elizabeth ta kwana a asibiti don gudanar da bincike kan yanayin lafiyarta, bayan likitocin sun bata shawarar soke yin tafiya zuwa Ailan Ta Arewa.

Kungiyar yan jarida ta kasar ta ba da rahoton cewa har zuwa daren Laraba sarauniyar na a asibitin King Edward da ke tsakiyar birnin London.

Kamfanin dillancin labaran Burtaniya ya ce ya fahimci cewa lamarin bai da wata alaka da cutar korona.

A yanzu fadar ta tabbatar da cewa ta koma gida cikin koshin lafiya.

A farkon wannan watan ne aka ga sarauniyar mai shekara 95 da ke zaman shugabar gwamnatin kasar na dogara sanda, yayin da take halartar wata coci da ke Westminster.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *