fbpx
Friday, January 21
Shadow

Sarkin Ban Kano Alhaji Mukhtar Adnan ya rasu

Sarkin Ban Kano Alhaji Mukhtar Adnan ya rasu yau Juma’a da Asuba.

Marigayin ya rasu yana da shekara 95 a duniya.

Daya daga cikin ‘ya’yansa Baba Ado ne ya tabbatar wa da BBC labarin rasuwar tasa.

Ya ce ya rasu ne dab da asubahin ranar Juma’a a sibitin UMC Zahir da ke unguwar Jan Bulo inda ya yi jinya.

Za a a yi jana’izarsa bayan Sallar Juma’a a babban masallacin garin Dambatta, da ke jihar Kano.

Alhaji Mukhtar Adnan yana daga cikin masu zaben Sarkin Kano wanda shi kadai ne ya zabi sarakunan Kano guda hudu da suka hada da Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Inuwa da Alhaji Ado Bayero a 1963, da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a 2014 da kuma Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a 2020.

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ne ya nada shi Sarkin Ban Kano kuma Hakimin Dambatta a shekarar 1954.

An haifi marigayin a watan Janairun 1926.

Ya rasu ya bar ‘ya’ya da dama cikinsu har da Dakta Mansur Mukhtar, tsohon Ministan Kudi na Najeriya, wanda kuma a yanzu mataimakin shugaba ne a Bankin Musulunci na Duniya da ke da cibiya a kasar Saudiyya.

An zaɓe shi ɗan majalisar wakilai a jamhuriya ta farko ƙarƙashin jam’iyyar NPC daga 1959 har zuwa 1966 lokacin da sojoji suka yi juyin mulki na farko.

Ya zama mai tsawatarwa a Majalisar Wakilai ta Lagos a jamhuriya ta farko.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *