fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Sarkin Gaya, Alhaji Dr. Ibrahim Abdulkadir, ya rasu

Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulkadir, ya rasu a jihar Kano ranar Laraba.

Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya tabbatar da mutuwar a wani rubutu da ya wallafa a Facebook.

Ya wallafa, “Kamar yadda Abubakar Aminu Ibrahim, SSA ya sanar da Gwamnan Jihar Kano, Sarkinmu na Masarautar Gaya, Alhaji (Dr.) Ibrahim Abdulkadir ya rasu, ‘Inna lillahi wa inna ilaihi raji’ ba ‘!

“Sarki babban jagora ne, an haife shi a shekarar 1930, shekaru 91 da suka gabata, kuma ya yi sama da shekaru 30 a kan karagar mulki.

“Allah (SWT) ya karbi ayyukansa na alheri, ya ba shi Jannah Al-Firdausi, ya baiwa iyalansa da daukacin masarautar Gaya karfin gwiwa don jure wannan babban rashi. Ameeen! “

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *