fbpx
Monday, September 27
Shadow

Sarkin Kontagora, Alhaji Saidu Umaru Namaska ​​ya rasu

Sarkin Sudan na Kontagora, Jihar Neja, Alhaji Saidu Umaru Namaska, ya rasu.

Dattijon mai shekaru 84, wanda ya shafe shekaru 47 a kan karagar mulki, ya rasu a asibitin Abuja, inji rahoton Daily Trust.

Haka zalika, babu wata sanarwa a hukumance da ta fito daga dangin da fadar amma wata majiya ta tabbatar da rasuwar sarkin.

Mutuwar tasa na zuwa ne watanni uku bayan da ‘yan bindiga suka kashe dansa, Alhaji Bashar Saidu Namaska, a lokacin da suka kai hari a gonar sarkin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *