fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Sarkin Musulmi yayi Allah wadai da sabuwar Rundunar tsaron da matasan Arewa suka kirkiro ta Shege Ka Fasa

Me Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na III ya zargin manyan Arewa da Zurawa wasu matasan yankin Ido inda suka bullo da wata Rundunar tsaro da suka sakawa Suna Shege Ka Fasa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Sarkin Musulmin ya bayyana hakane a Ranar Alhamis wajan taro kan tsaron yankin Arewa daya gudana a Kaduna.

Gamayyar wasu kungiyoyin matasan Arewa ne suka fito da wannan rundunar tsaro a matsayin martani ga rundunar tsaron yankin Yarbawa ta Amotekun da ta jawo cece-Kuce

Da yake magana a wajan Taron, Sarkin Musulmi yace, nagani a Talabijin kuma lamarin ya dauki hankalin kafofin watsa labarai kuma manya suna ganin matasan amma sun kyale. Ya kara da cewa to dan haka manyanmu da masu fada aji sune matsalar. Idan basu shigewa matsa gaba ba matasan zasu rika yin abune suna ganin kamar daidai suke yi.

Dolene a jawo hankalin Matadannan ta hanyar shige musu gaba da jagoranci me kyau. Yace yanzu sun kaddamar da tundunar tsaronsu da suka sakawa Shege Ka Fasa, Me hakan ke nufi?

Yace yana baiwa manyan Arewa shawarar da su jawo hankalin matasannan, kada su bari su kwace ragamar shugabanci daga hannunsu. Yace ya kamata a jawo kowa a jiki duk kuwa kankantarshi.

Sarkin Musulmi ya jawo hankalin gwamnonin Arewa da su yi maganin matsalar tsaron da ake fama da ita a yankin, ya kuma jawo hankali kan marayu dubu 50 da suka samu sanadiyyar tikicin Boko Haram inda yace a yi wani abu akai in ba haka ba, nan gaba wadannan marayu zasu iya komawa wata matsalar da ta fi ta Boko Haram.

Yace ana bayar da shawarwari da yawa mamma ba’a amfani da su. Idan kuwa haka ta ci gaba to zamu ci gaba da ganin matsaloli.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *