fbpx
Thursday, July 29
Shadow

Sarkin Musulmi yayi kira da ayi addu’a don kawo karshen rashin tsaro a kasar nan

Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar wanda ke jagorantar Jama’atu Nasril Islam ya bayyana a matsayin “abin takaici” ci gaba da rashin tsaro da ke addabar yan najeriya wanda ya hada da ’yan fashi da satar mutane da tayar da kayar baya a wasu sassan arewacin kasar.

JNI din ta lura cewa ci gaba da rashin tsaro a fadin Arewa ba tare da wata mafita ba, abin Allah wadai ne, tare da yin kira ga ‘yan Nijeriya da su ba da bayanan sirri ga jami’an tsaro don kawo karshen kalubalen tsaro.

Kungiyar Musulmin ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Sakatare Janar na JNI, Dr Abubakar Khalid-Aliyu, mai taken, ‘Sanarwar da aka fitar a ranar 19 na farkon Dhul-hijjah 1442AH (2021) da kuma bukatar ci gaba da addu’o’i da kyawawan halaye na ibada.

Jama’atu Nasril Islam karkashin jagorancin Mai martaba, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, Sarkin Musulmi, yana kira ga al’ummar Musulmin Najeriya da su kara himma da jajircewa wajen ayyukan alkhairi a wadannan ranakun da suka fara. jiya, lahadi, 11 ga watan yuli, 2021.

“Don haka muke amfani da wannan lokacin don yin kira ga al’ummar Musulmi da su yi koyi da yafiya kuma su guji aikata abin da zai jawo fushin Allah (SWT).

“Ya kamata dukkanmu mu kasance masu karamci a sadaka kuma ya kamata mu himmatu da addu’oi domin kawo karshen tarin kalubalen da ke addabar kasar Najeriya.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *