fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Satar Dalibai a Kagara jihar Naija ya nuna Gwamnati bata koyi darasi daga Satar Daliban Kankara ba>>’Yan Najeriya na caccakar Gwamnati

A yaune aka tashi da bakin Labarin cewa an sace dalibai da ba’a san yawansu ba da kuma malamai a makarantar Sakandare ta Kagara dake karamar hukumar Rafi ta jihar Naija.

 

Wannan na zuwane watanni kadan bayan irin haka ta faru a jihar Katsina, Mahaifar Shugaban kasa, Muhammadu Buhari inda aka sace dalibai daga makarantar Kankara.

 

Wasu ‘yan Najeriya sun hau shafukan sada zumunta inda suka rika bayyana rashin jin dadinsu akan wannan lamari.

 

Sanata Shehu Sani na daga cikin wanda suka nuna bacin Ransu akan wannan lamari inda ya Rubuta a shafinsa na Twitter cewa, Iyaye na ta dauke ‘ya’yansu daga makarantar Kagara inda aka sace daliban da ba’a san yawansu ba sannan kuma ba’a san inda suke ba. Ya kara da cewa hakan na nuni da ba’a koyi darasin kkmai ba daga irin haka data faru a Kankara ba.

 

Parents are just pulling out their Children from the Govt Science College Kagara,the scene of the early morning invasion by Bandits. One student is confirmed killed.The whereabouts & numbers of those abducted remains Unknown. No lessons learnt from Kankara.

 

 

Shima me sharhi akan al’amuran yau da kullun kuma Lauya, Bulama Bukarti ya bayyana cewa Rahoto mara dadi na sace dalibai a Kagara jihar Naija. Yace kamar dai yanda ya faru a Kankara, sun jene da kayan Sojoji makarantar dake da Dalibai 1000. Yace wasu sun tsere amma ba’a san yawan daliban da malaman da aka sace ba. Yace ba’a koti darasin komai daga Abinda ya faru a Kankara ba.

 

Unsettling reports of another mass kidnapping this time in Kagara, Niger State. Strikingly identical to Kankara. Gunmen in security uniforms invaded GSC Kagara with ≈1,000 pupils. Some have escaped. No figures of those abducted including teachers. We learnt NOTHING from Kankara.

 

 

Shima wani Deji Adesogan dake sharhi akan al’amuran yau da kullun ya bayyana cewa hakan na zuwane watanni kadan bayan da irin haka ta faru a Kankara. Ya bada shawarar dakatar da makarantun kwana a Arewacin Najeriya.

 

Personally I’m not happy cos the #KagaraBoys abduction is happening few months after Kankara boys abduction. My clarion call today is for FG & Northern Govs to see reason(s) that running boarding schools in the northern region means exposing students to avoidable security threats.

 

 

 

https://twitter.com/_isahhabib/status/1361993737832964096?s=19

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *