fbpx
Monday, May 10
Shadow

Saurayi ya kashe Budurwarsa saboda ta ki yadda yayi lalata da ita

Wani mutum dan Shekaru 42 ya kashe budurwarsa da Hamma saboda wai ta ki yadda yayi lalata da ita.

 

Mutumin me suna Papa Gyabi ya aikata lamarinne a ranar Asabar, 24 ga watan Afrilu a yankin Shama Khumasi dake kasar Ghana.

 

Budurwarsa me suna Rita ta kai masa ziyara ne a gida inda kuma da dare yayi suka shiga daki, amma ta ki yadda ta biya masa Bukata, sun yi ta fada tsakar dare, inda daga baya aka ji shiru. Wani makwabcinsu, ya shaidawa Graphic Online cewa, da ya ji shiru shine ya leka ya ga me ya faru.

 

Koda ya leka sai ga budurwar kwance cikin jini. Ya garzaya wajan ‘yansandan Sharma inda ya kai musu Rahoto. Kakakin ‘yansandan, DSP Olivia Adiku ya tabbatar da faruwar Lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *