Wednesday, 9 October 2019

Yawan Haihuwa yana kawo Sankarar Mahaifa>>Inji Matar Gwamna

Masu bincike sun ce cutar cancer ko sankarar mahaifa ta fi tsanani a arewacin Najeriya saboda yawan haihuwa, a cewar matar gwamnan jihar Kebbi a Najeriya.

Tuesday, 8 October 2019

Ya Sayi Gidan Giya Ya Mayar Da Shi Makarantar Addini Da Na Zamani A Jihar Yobe

BABBAN JIHADI
Makarantar Ubayyu Ibn Ka'ab wata makaranta ce da a shekarun baya take zaman wani gagarumin gidan giya wanda yayi kaurin suna sosai a fadin garin Gashua da kewaye wajen ayyukan ashsha.  

Matashin Da Ya Yi Mafarkin Gwamna Elrufai Ya Soma Farin Jini, An Ba Shi Kyautar Sabon Babur

Matashin nan mai suna Nazifi Zubairu wanda aka fi sani da Zuri, wanda ya bayyana cewa ya yi mafarkin gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Elrufai ya soma samun farin jini a wasu sassan kasar nan, inda yake ta shan kiran daga wasu jihohi da suka hada da Kano, Kaduna Lagos, Katsina, Niger, Zamfara, Sokoto, Abuja da sauran su domin jin irin mafarkin da ya yi kan gwamnan.

Kalli kayatattun hotunan yanda shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudi ga majalisa

Wasannan kayatattun hotunane da suka nuna yanda shugaban kasa, Muhammadu Buhati ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2019 ga majalisun tarayya a tau, Talata.

Tsohon gwamnan Katsina, Shema ya bayyana a kotu kan zargin Almundahanar kudi

Isowar Tsohan Gwamnan Jihar Katsina, Barista Ibrahim Shehu Shema Babbar Kotun Tarayya, Dake Katsina. Bisa Zargin Almundahanar Bilyan Biyar Kudin Sure-P. Bayan Zaman Kotun na Yau, Mai Shariah Ta Dage Zuwa 30-10-2019 Domin Cigaba Da Shariar.

Rahoto kan yadda shugaba Buhari ya mika kasafin kudin 2020 ga majalisa

Wasu 'yan majalisa sun kaure da kiran 'Sai Baba' lokacin da Shugaba Buhari ya isa zauren majalisar wakilan kasar.

'Yan bindiga sun sace mutum 9 a Abuja

Rahotanni na cewa an sace wasu mutum tara, ciki har da yaro dan shekara 12 a unguwar Pegi da ke yankin Kuje a babban birnin Najeriya, Abuja.

Za'a fara kirar Mota 'yar Najeriya da mutum zai dauki shekaru 5 yana biya

Mota Kirar Nijeriya Ta Kusa Fitowa, Inda 'Yan Nijeriya Za Su Saye Ta Bashi Su Biya Cikin Shekaru Biyar, Cewar Gwanin Kera Mota, Jilani Aliyu.

Kalli hotunan Diyar Gwamnan Zamfara da Angonta da aka yi aurensu kwanannan

Wadannan hotunane daga wajan bikin diyar gwamnan jihar Zamfara, Rukayya Bello Matawalle da Angonta, Mukhtar da aka yi a makon daya gabata.

Gwamna Masari Ya Nada Mataimakinsa Na Musamman Kan Mawakan Zamani

Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya nada Ukashatu Suleman, wanda aka fi sani da Ajuba a matsayin mataimaki na musamman kan mawakan zamani.

Shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2020 ga majalisa

A yau Talatane shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai gabatarwa da majalisar tarayya kasafin kudin shekarar 2020.

Gareth Bale yana 'fushi da Real Madrid, yana so ya bar su'

Dan jaridar BBC Radio 5 Live, Guillem Balague, ya yi ikirarin cewa dan wasan gaba na Real Madrid Gareth Bale ya "fusata sosai" da kulob din kuma yana matukar son barinsu.

Labarin komawar tsabar kudi miliyan dari 9 takardu a ofishin EFCC:Hukumar ta mayar da martani

Wani labari ya rika yawo a shafukan sada zumunta cewa wasu kudi da yawansu ya kai Naira Miliyan 900 dake ajiye a ofishin EFCC sun bce inda suka koma takarda. Saidai a sanarwar data fitar, EFCC ta karyata wannan lamari.

An kashe mutane 4 ta hanyar bude a wata mashaya dake Amurka

Mutane 4 sun rasa rayukansu yayinda wasu 5 suka jikkata sakamakon bude wuta kan wata mashaya dake jihar Kansas din Amurka.

Barcelona ta kori koci kuma tsohon dan wasanta

Barcelona ta sallami kocin tawagar matasan ta ta ‘yan kasa da shekaru 19 Victor Valdes ba tare da bata lokaci ba, bayan rade – radin sa – in – sa tsakaninsa da daraktan matasa na kungiyar Patrick Kluivert.

Mabiya Darikar Tijjaniyya Sun Gina Katafaren Masallaci A Birnin New York DAKE Kasar Amurka

Al'ummar Tijjanawa mazauna kasar Amurka, dake birnin New York, sun gina wani katafaren masallaci, da aka kashe miliyoyin dalolin kudade yayin aikin ginin sa.

Jihohi 31 na fama da tsananin talauci a Najeriya>>Inji Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga ‘yan Najeriya attajirai da su duba yiwuwar bunkasa tattalin arzikin Najeriya ta hanyar mai da hankali wajen kirkiro sana’o’I, bunkasa harkokin kasuwanci, cinikayya da gina kasa Najeriya ta hanyar yin amfani da arzikin da Allah yayi wa kasar.

Binciken BBC ya bankado yanda Wasu malaman jami'a ke lalata da dalibai

Rashin sani ya wani babban malamin Jami’ar Legas kokarin yin lalata da wata yarinya da ta je a matsayin mai neman a dauke ta shiga jami’ar.

Real Madrid na son sayen Kante daga Chelsea

Kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid ta shirya tsaf domin takara da Juventus wajen kokarin sayo dan wasan Chelsea, N'golo Kante kamar yadda jaridar Mail ta rawaito.

Kalli Datijjon Da Ya Yi Sanadiyyar Musuluntar Mutane Sama Da Milyan Daya

ALLAHU AKBAR
Wannan datijjon sunan shi Deen Muhammad Shaikh dan kasar Indiya. Ya kasance mabiyin addinin Hindu masu bautar gumaka, daga baya Allah ya shiryar da shi zuwa addinin musulunci, ya musulunta a shekarar 1989, bayan ya  musulunta ya shiga harkar da'awa, an ce daga musuluntar sa zuwa yanzu ya jawo sama da mutane miliyan daya da duba takwas zuwa musulunci daga addinin Hindu.