Thursday, 7 November 2019

BAYAN RUFE BODA: An Hana Sayar Da Man Fetur A Gidajen Mai Dake Kusa Da Iyakokin Nijeriya

 Gwamnatin tarayya ta bakin hukumar hana fasa kwabri wato Kwastam, ta bada umurnin daina sayarwa gidajen mai dake kimanin kilomita 20 da iyakokin Najeriya man fetur. 

Ministan Sadarwa Sheikh Pantami Ya Dakatar Da Biyan Kudade A Ofisoshin Jakadanci

Gwamnatin Nijeriya ta ba da umarnin dakatar da biyan duk wasu kudade cikin gaggawa a duk ma'aikatun gidan waya na Najeriya, NIPOST.

Jihar Katsina ce ta fi mata da suka fi yawan haihuwa a Najeriya

Wani bincike da hukumar kula da yawan 'yan Najeriya, NPC da ma'aikatar Lafiya ta kasa suka gudanar ya bayyana cewa jihar Legas dake kundancin Najeriyace ke da mata wanda basu cika haihuwa da yawa a Najeriya ba inda binciken ya bayyana cewa akalla kowace mace na da 'ya'ya 3.4

Kalli yanda wata mata ta gagari sojoji biyu dake son ladaftar da ita

Wannan hotunan wasu sojoji mata 2 ne da Shafin Instablog ya ruwaito cewa suna kokarin hukunta wata mata amma ta gagaresu, hotunan sun dauki hankula a shafukan sada zumunta inda akaita bayyana mabanbanta ra'ayoyi akai.

Champions League:Real Madrid, Juventus da PSG sun kai matakin kungiyoyi 16

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta lallasa Galatasary da ci daidai har 6-0 a wasan da suka buga a daren jiya na gasar Champions League wanda wannan nasara ta baiwa Madrid din damar zuwa matakin kungiyoyi 16 a gasar na kifa daya kwala.

Daya cikin takwas na yara kanana a Najeriya na mutuwa kafin cika shekaru 5

A Najeriya daya cikin takwas na yara kanana na mutuwa kafin cika shekaru 5 da haihuwa a duniya.

Jami'an 'Yan Sanda Da 'Yan Banga Sun Budewa Masu Kasa Kayan Sana'a A Bakin Titin Mararraba/Nyaya Wuta

Rahotanni daga garin Mararraban Nyaya sun tabbatar da cewa jami'an 'yan sanda da na 'yan banga sun bude wuta kan masu kasa kaya a bakin babban titi, inda har ta kai ga an raunata mutane da dama.

JIGAWA: Bakin makiyaya sun fatattaki ‘yan sanda, sun mamaye gonakin manoma

Wani gungun makiyaya dauke da makamai sun raunata wani jami’in dan sanda yayin da suka kai wa jerin motocin jami’an hari a Karamar Hukumar Kirikasamma, Jihar Jigawa.

BADAKALAR SATAR MUTANE: An Kama Matasan Da Suka Shirya Zanga-zangar Lumana A Majalisar Kaduna

'Yan sanda sun kama wanda suka yi zanga-zangar lumana  a kofar majalisar jihar Kaduna. 

Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila Ya Sayawa Iyayen Jaririya Dake Sansanin Gudun Hijira Gida A Katsina

Idan za ku iya tunawa cewar a ranar Litinin 16 ga watan Satumbar 2019 ne mai girma kakakin majalisar wakilan Najeriya Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya ziyarci jihar Katsina, kamar yadda Hamza Ibrahim Baba mataimaki na musamman ga shugaban majalissar wakilai Hon. Femi Gbajabiamila a bangaran tallafa 'yan gudun hijira, ya ce a wannan rana suka ziyarci daya daga cikin sansanonin ƴan gudun hijirar da ke cikin garin Katsina 

Faransa na zawarcin 'yan ci-rani domin ba su aiki

Gwamnatin Faransa ta bayyana wani shirin karbar ‘yan ci-rani da ke da kwarewa a fannoni daban-daban, tare da ba su damar samun ayyukan yi a cikin kasar, shirin da zai fara aiki a farkon shekara mai zuwa.

Kano ne birni mafi gurbacewar iska a Afirka>>Rahoto

Rahoton dai ya ce birnin Kano ne ke da mafi gurbacewar iska a fadin nahiyar Afirka, inda gurbacewar iskar ta kai kashi 53.4 cikin dari.

Wednesday, 6 November 2019

Kwana daya bayan mai aikin Mummunan raunin da ya ji, An sallami dan wasan Everton, Gomez daga Asibiti

Kwana daya kacal bayan mummunan raunin da tauraron dan kwallon kasar Portuga me bugawa Everton wasa dan shekaru 26 ya ji a wasan da suka buga da Tottenham da ya kare da sakamakon 1-1, An sallameshi daga asibiti.

An tube Xhaka Kaftin na Arsenal an ba Aubameyang

Kocin Arsenal Unai Emery ya tube Granit Xhaka a matsayin kaftin inda ya nada Pierre-Emerick Aubameyang

Fasto Chris ya gina Katafaren Makaranta Da Asibiti domin tallafawa a jihar Adamawa

Shugaban cocin Christ Embassy, Fasto Chris Oyakilome ya gina asibiti da makaranta a garin Demsa dake jihar Adamawa domin tallafawa marasa karfi. Inda za a dinga jinya da karatu kyauta.

Ga Abinda Ake yi da kudin Fatun Layya da kungiyar Izala ke karba

Wannan hoton aikin ginin babban masallacin Juma'a na Izala dake hedikwatar Izala dake Utako, Abuja karkashin jagorancin Sheik Dr. Abdullahi Bala Lau.

Nijeriya Za Ta Fara Fitar Da Shinkafa Zuwa Kasashen Waje Nan Bada Jimawa Ba>>Dangote

Kungiyar Dangote ta dauki alkawarin sauya Nijeriya daga wata kasar da ke shigo da shinkafa zuwa babbar kasa mai fitar da abinci zuwa  kasashen waje.

Champions League: Liverpool ta buga 21 da Genk: Haaland ya kafa tarihin da babu me irinshi

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta buga 2-1  da Kungiyar Genk a wasan da suka yi a daren jiya na gasar cin kofin Champions League. Wijnaldum da Chamberlain ne suka ciwa Liverpool kwallayenta.

An nuna wa Osinbajo wariya a gwamnatin Buhari>>Kungiyar kare muradun yarbawa

Wasu ƙungiyoyi a Najeriya sun yi zargin cewa ana mayar da mataimakin shugaban ƙasar Farfesa Yemi Osinbajo ɗan kallo a tafiyar da al'amuran ƙasa.

AKWAI MATSALA FA: Matashi Ya Yi Wanka Da Ruwan Kwata Saboda Murnar Ganduje Ya Baiwa Murtala Sule Garo Kwamishina

Shi ma ga wani matashin masoyin Hon. Murtala Sule Garo da aka nuno shi cikin faifain bidiyon yana wanka da ruwan kwata saboda murnar an sake naɗa shi kwamishina.