Monday, 2 December 2019

Mufti Menk ya kaiwa A'isha Buhari ziyara a fadar Gwamnatin tarayya

Uwargidan shugaban kasa, Hajiya A'isha Buhari ta karbi bakuncin shahararren malamin addinin islama dan kasar Zimbabwe,Isma'il Mufti Menk a fadar gwamnati dake babban birnin tarayya, Abuja.

Kalli yanda dan sanda sanye da kayan aikinshi ya shiga aka yi aikin gyara makabarta dashi

ALLAHU AKBAR

Wani jami'in Dan Sanda Kenan Da Ya Shiga Cikin Tawagar Masu Aikin Gayyar Sharar Makabarta A Garin Bauchi.

Dalilin da ya sa majalisar mu ta ki amince wa Buhari ya ciwo bashin biliyoyin daloli>>Sanata Shehu Sani

Tsohon Sanatan dake wakiltar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani, ya bayyana cewa babban dalilin da ya sa majalisar da ta gabata ta ki amince wa Bubari ya ciwo bashin biliyoyin daloli shi don ta ceto Najeriya daga sarkakin bashi.

Mutane na caccakata ne saboda abinda mahaifina yayi>>Zahara Buhari

Diyar shugaban kasa,Zahara Buhari ta bayyana cewa da yawan wadanda suke caccakarta da kaya mata kalaman da basu dace ba a shafukan sada zumunta suna yi ne saboda wasu abubuwa da mahaifinta, shugaban kasa,Muhammadu Buhari yayi.

Sunday, 1 December 2019

Messi ya ciwa Barca kwallo 1 data bata nasara akan Atletico Madrid

A yayin da wasa yayi zafi tsakanin Barcelona da Atletico Madrid, Golan Barca Ter Stegen ya taimakawa kungiyar sosai a zagayen farko kamin a je hutun rabin lokaci inda ya tare kwallaye kusan 2 masu kyau wanda da yayi sakwa-sakwa dasu da sun shiga raga.

Dan wasan Najeriya ya taimakawa Leicester City komawa matsayi na 2 a Teburin Premier League, Arsenal kuwa bata cannja Zani ba

Tauraron dan kwallon Najeriya dake bugawa Leicester City wasa, Ihaenacho ya taimakawa kungiyar yin nasara a wasanta na yau inda ya bayar da taimako aka ci kwallo ta farko sannan shima ya ci kwallo ta 2.

Tauraruwar fina-finan Najeriya ta sha alwashin wulakanta Qur'ani

Wata fitsararriyar tauraruwar fina-finan Kudu me suna Etinosa da a kwanakinnan ta wulakanta littafin Baibul ta hanyar yin amfani dashi a matsayin abin kakkabe tokar taba ta sha alwashin wulakanta Qur'ani.

Gwamnan Jahar Kebbi Sanata Bagudu Ya Mika Yaron Da Aka Sace Ga Iyayensa

Gwamnan jahar Kebbi Sanata Atiku Bagudu ya mika yaron da aka sace hannun iyayen shi bayan kwashe watanni uku hannu masu satar yara.

YABON GWANI YA ZAMA DOLE: AMFANIN DA MALAM AMINU DAURAWA KEWA AL-UMMA

Babu shakka samun Mutane irinsu Malam Shiekh Muhammad Aminu Daurawa a cikin wannan al'umma babban alkairi ne gami da rahama da jin kai daga wajen Allah, da yawan mutane basu san irin alkhairin da wannan bawan Allah ke aiwatarwa ba, wanda zan iya cewa bansan wani malami a ƙasar nan da zaiyi kunnen doki da Malam daurawa  wajen amfanar da al'umma ba.

ABIN MAMAKI: Mahaukaciya Ta Taya Shi Murnar Kammala Karatu

Wata mahaukaciya na daga cikin wadanda suka taya wani matashi mai suna Bashir Omobolaji Abdurraheem murnar kammala karatu da ya yi a makarantar Nasarawa Poly dake garin Lafiya babban birnin jihar Nasarawa a ranar Alhamis din da ta gabata.

Matar Gwamnan Sokoto Ta Ziyarci Kabarin Sheikh Ahmad Tijjani

Matar Gwamnan jihar Sokoto Hajiya Maryam Mairo Aminu Waziri Tambuwal ta ziyarci kabarin fitaccen malamin Addinin Musulunci, Marigayi Sheikh Ahmad Tijjani.

Karamin Yaron Da Yake Amfani Da Goran Madara Yana Kirkirar Fitila Mai Hasken Awa Biyar

FASAHA:
Wannan shine 'Dalibi Ibrahim Yakubu Muhammad, mazaunin garin Rinjin Gani daga karamar hukumar Toro jihar Bauchi.

Buhari Zai Gina Sabuwar Jami’ar Rundunar Sojan Sama A Jihar Bauchi

 Gwamnatin Nijeriya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta gina katafaren jami’ar rundunar Sojan sama a garin Bauchi na jahar Bauchi kamar yadda babban hafsan sojan sama ya tabbatar.

Yadda Al'ummar Kauyen Runjin Dutsi Suka Ginawa 'Ya'yansu Makarantar Firamare Da Kansu

KALUBALE GA GWAMNA TAMBUWAL NA SOKOTO

Mutanen kauyen Runjin Dutsi kenan dake gundumar Sanyinnawal a karamar hukunar Shagari ke aikin gina makarantar firamare ta hanyar aikin gayya.

Abinda ya faru tsakanin Lewandowski da Bayer leverkusen ya dauki hankula

Kungiyar kwallon kafa ta Bayer Munich ta sha kashi a hannun Bayer Leverkusen da ci 2-1 a wasan da suka buga jiya na gasar cin kofin Bundesliga na kasar Jamus.

Sojojin Najeriya da hadin gwiwar na makwabtan kasashe sun kashe Mayakan Boko Haram 13

Hadin gwiwar dakarun Najeriya da na kasashen yankin tafkin Chadi sun sake samun wani gagarumar nasara a wata fafatawa da suka yi a Arewacin jihar Borno.

Hafsat Idris ta haskaka sosai a wadannan hotunan nata

Tauraruwar fina-finan Hausa  Hafsat Idris kenan a wadannan hotunan nata data sha kyau, tubarkallah muna mata fatan Alheri.

Real Madrid ta hau na 1 a Teburin La liga: Ramos yaci mata kwallo sannan ya jawo an ci ta

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta yiwa Deportivo Alaves ci 2-1 a wasan da suka buga jiya na gasar cin kofin La liga na kasar sifaniya. Dan wasan baya, Sergio Ramos ne ya fara ciwa Madrid kwallo inda Carvajal ya ci ta 2.

Taron Ganawa da Zahara Buhari me kudin shiga Dubu 10 daya jawo cece-kuce ya kammalu

Taronnan na ganawa da diyar shugaban kasa, Zahara Buhari Indimi da ya jawo cece-kuce sosai a shafukan sada zumunta saboda kudin shiga da amasa na Naira dubu 10 ya kammalu.

Liverpool ta kara bada tazara a Teburin Premier League: Chelsea da Man City sun rasa maki

Liverpool ta yiwa Brighton ci 2-1 a wasan da suka buga jiya na gasar con kofin Premeir League na kasar Ingila inda da wannan nasara suka bayar da tazarar maki 11 a saman teburin Premier League.