Thursday, 13 February 2020

Ban san iya yawan kayan sawata ba>>Hadiza Gabon

Tauraruwar fina-finan Hausa,Hadiza Gabon ta bayyana cewa babban burinta nan da shekaru 5 shine yin aure, haihuwa da Arziki.

Majalisar Dattijai ta bukaci hukumar soji ta kafa Rundunar musamman a Auno, Jihar Borno

A zamanta na yau,Majalisar dattijai ta yi Allah wadau da harin da Boko Haram ta kai Garin Auno na Maiduguri wanda rahotanni suka bayyana cewa ya kashe mutane 30.

'Yan Najeriya basu faye amfani da Kwaroron robaba wajan Jima'i ba

Wani sabon bincike ya nuna cewa kashi 34 cikin 100 ne kadai na 'yan Najeriya suke amfani da kwaroron roba yayin jima'i, kuma cikin wannan yawan kashi 28 cikin 100 ne kawai ke amfani da shi ko yaushe.

Allah ya karbi ransa bayan yayi Alwala ya kama hanyar zuwa Masallaci

INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN

Sayyadi Rabiu mutumin kirki ne mai yawan ibada, kullum hannun shi da carbi yana wuridi. Ba jinya ba komai ya yi wanka ya yi alwala zai tafi masallaci kawai zai tsallaka tshohuwar rijiyar dake gidansu ya taka bakin murfin rijiyar bisa kaddara murfin rijiya ya juya da shi ciki. Kafin hukumar kwana-kwana su iso ya cika.

Kotun koli ta soke zaben gwamnan Bayelsa na APC

Kotun kolin Najeriya ta soke zaben gwamnan jihar Bayelsa da ke kudu maso kudancin kasar.

Hotonnan na uhuhu, diya, jika, da kaka ya dauki hankula

Hotonnan na iyalai su 4 ya dauki hankula sosai a shafukan sada zumunta inda akai ta yabawa dashi. Muna musu fatan Alheri.

Ba yadda za'a yi Boko Haram su rika kawo hari ba tare da sanin ku ba>>Shugaba Buhari ya gayawa shuwagabannin al'ummar Borno

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga mutanen jihar Borno da su hada kai da sojoji da sauran hukumomin tsaro don saukaka nasarar aiwatar da yaki da 'yan tawayen.

Ya Kammala Rubuta Alkur'ani Bayan Shafe Sama Da Shekaru Yana Aikin Rubutawa

Malam Abubakar Kenan Mazaunin Unguwar Darmanawa a Kano, 'yan uwa da abokan arziki sun yi ta zuwa wurin sa don taya shi murnar rubuta sabon Kur'Anin da ya yi bayan shafe kusan shekaru biyu yana rubutunsa.

An gano man fetur me yawan ganga Biliyan 1 a Arewa

Karamin ministan Albarkatun man fetur,Timipre Sylva ya bayyana cewa an gano mai me yawan ganga Biliyan 1 a yankin Arewa maso gabas.

Gobara ta tashi a gidan tsohon shugaban kasa, Obasanjo

Gidan tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo yayi gobara. Gidan dake birnin Abeokuta na jihar Ogun ya kama da wutane da misalin karfe 10 na daren Laraba.

Janar Murtala Mohammed ya cika shekara 44 da rasuwa

Ranar Alhamis, 13 ga watan Fabarairun 2020 tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya, Janar Murtala Ramat Mohammed ke cika shekara 44 da rasuwa.

Joseph Yobo ya zama Mataimakin Kocin Super Eagles

Hukumar Kwallon Najeriya, NFF ta zabi tsohon dan wasan Najeriya, kuma tsohon kyaftin din kasar, Joseph Yobo a matsayin Mataimakin Kocin ’yan kwallon Najeriya, wato Super Eagles.

Kayatattun Hotunan Yawan Shakatawar 'yan kwallon Arsenal a Dubai

Bayan hutun da aka samu a gasar Premier league, 'yan wasan kungiyar Arsenal sun tafi hutu kasar Dubai.

Adam A. Zango da Rahama Sadau sun haskaka a wadannan hotunan

Taurarin fina-finan Hausa, Rahama Sadau tare da abokin aikinta, Adam A. Zango kenan a wadannan hotunan nasu da suka haskaka, tubarkallah, muna musu fatan Alheri.

Barcelona: Dambele zai yi jinya ta tsawon watanni 6

Kungiyar kwallon kafa ta Spaniya Barcelona ta bayyana cewar dan wasanta dan kasar Faransa Ousmane Dambele zai dauki tsawon watanni 6 yana jiyya sakamakon tiyata da aka yi masa bayan raunin da ya samu a cinyarsa ta dama.

Wasu 'Yan Jihar Borno Ba Su Ji Dadin Ziyarar Shugaba Buhari Ba, yawanci fuskar mutane ba annashuwa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa birnin Maiduguri dake jihar Borno bayan dawowarsa daga taron kolin kungiyar hadin kan Afrika da ake kira AU a takaice, wanda aka yi a kasar Habasha. Shugaban ya kai wannan ziyarar ne don jajantawa al’ummar jihar biyo bayan wani mummunan hari da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai a garin Auno wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 30 da kuma kone konen motoci da gidaje.

Chelsea na daf da sayen Hakim Ziyech daga Ajax

Tattaunawa ta yi nisa tsakanin Chelsea da Ajax kan sayen dan wasan gaba Hakim Ziyech a wannan kaka kan kudi fam miliyan 38, kuma nan ba da dadewa ba zaa sanar da kammaluwar cinikin.

Buhari ya ji ihun da aka masa a Maiduguri: Ji martanin daya mayar

Fadar shugaban Najeriya ta ce ta ji yadda wani rukunin mutane suka yi wa tawagar shugaba Buhari ihu a yayin da ya kai ziyarar jaje a Maiduguri.

RAHOTON MUSAMMAN: An fallasa yadda Diya, Aziza da Magashi suka tafka satar bilyoyin nairori

Rahotannin musamman sun bayyana yadda wasu manyan sojoji a lokacin mulkin marigayi Sani Abacha, suka bi sahun sa wajen jidar bilyoyin kudaden al’umma su na maidawa na su.

Ya Rasu Bayan Ya Bada Hantar Sa Don Ceto Rayuwar Mahaifiyarsa


Muna yawan jin labarin son da uwa take yi wa ‘ya’yanta, sai dai a wannan lokacin ba son uwa bane, soyayyar da ne ga uwa.