fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Shahararren Mawaki, Idris Abdulkarim ya sake yin wakar Jaga-Jaga, Ministan Buhari yayi martani

Tauraron Mawaki, Idris Abdulkarim ya sake yin wakar Najeriya Jaga-Jaga da yai a baya.

 

A cikin wakar tasa, ya saka sunan karamin Ministan Kwadago, Festus Keyamo inda yacw shima ya shiga Gwamnati ana ci dashi.

 

Wannan dalili yasa Ministan Kwadagon ya fito yayi magana. Yace a lokacin da suke yakin neman zaben Shugaba Buhari, Idris Abdulkarim yayi ta neman ya ganshi dan ayi wannan tafiya tare.

 

Keyamo ya saka Hotunan irin sakonnin da Idris ya rika tura masa, yace a karshe dai sun hadu, inda Idris din yace yawa Shugaba Buhari wata waka kuma yanaso ayi amfani da ita. Saidai ya gayawa Idris cewa bashi da kudin da za’a yi aikin wannan waka domin shi sa kansa ne yake wannan aiki.

 

Yace daga baya Idris ya bayyaa masa cewa yana bukatar bashin kudi Miliyan 1.3 daga wajansa dan ya biya kudin Otal din da ya zauna sannan kuma Akwai mahaifiyarsa da bata da lafiya da yake son zuwa ya ganta.

 

Keyamo yace a karshe Idris ya nemi ya hadashi da Amaechi da Abubakar Malami. Yace daga karshe dai da ya ga ba zai samu abinda yake so ba, shine ya je ya koma bangaren Atiku, haddashi aka rikawa Gwamnatin Buhari Zanga-zanga.

 

Keyamo yace dashi da wasu kafan dake cikin gwamnati wanda zai iya bayar da shaida akansu, suna aiki ne dan yiwa jama’a hidima amma ba dan tara abin Duniya ba.

 

 

https://twitter.com/fkeyamo/status/1386071456564531203?s=19

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *