fbpx
Monday, November 29
Shadow

Shehin Malami Ya Ki Karbar Kyautar Motar Da Dan Majalisar Tarayya Ya Ba Shi, Inda Ya Ce Ya Je Ya Taimakawa Mabukatan Mazabarsa

Jigo a kungiyar addinin musulunci ta Ansarudden, Sheik Ahmed Abdulrahman ya ki karbar kyautar motar da dan majalisar tarayya mai wakiltar yakin Mushin dake jihar Lagos, wato Honatabul Bolaji Yusuf Ayinla ya ba shi.

Dan majalisar ya baiwa Shehin Malamin motar ne da nufin saukaka masa zirga-zirga. Amma sai Sheik Ahmed ya cewa dan majalisar ya rike motar, maimakon yi masa kyautar ya je ya ci gaba da kula da hakkin mabukatan dake mazabarsa. 
Shehin Malamin ya kuma yi wa dan majalisar tunatarwa kan muhimmancin kula da hakkin wadanda yake shugabanta.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *