fbpx
Thursday, July 29
Shadow

Shehu Sani yayi Allah wadai da sace sarkin Kajuru da ‘yan bindiga suka yi a jihar Kaduna

Shehu Sani, tsohon dan majalisar dattawa, ya koka kan hare-hare da sace-sacen mutane da ‘yan fashi ke yi a jihar Kaduna.

Tsohon dan majalisar, wanda ya wakilci gundumar Sanatan Kaduna ta Tsakiya a majalisa ta 8, yana maida martani ne game da sace Sarkin Kajuru, Alhaji Alhassan Adamu, da wasu danginsa 12.

‘Yan fashin, da yawa, sun mamaye fadar Kajuru na sarkin, tsakar daren Asabar inda suka yi ta harbi lokaci-lokaci don tsoratar da mutane kafin su sace mutanen.

Da yake tabbatar da satar mai martaba, jikansa, Dan Kajuru, Saidu Musa, ya ce “‘yan bindigar sun afka gidan ne da misalin karfe 12.30 na safe suka tafi da mai martaba da wasu danginsa goma sha biyu.”

Da yake maida martani game da wannan mummunan labari, Sani ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, “Sarkin Kajuru, tafiyar minti 30 daga Kaduna kuma an yi garkuwa da’ yan uwansa goma sha biyu da daren jiya.

“’Yan Bindigar sun yi aiki na tsawan awa guda a cikin Jiha ta ta Kaduna. A zamanin yau, ba batun wanda ya ke cikin lafiya bane, amma wane ne wanda za a afkawa na gaba”.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *