fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Sheikh Gumi ya kaiwa Fulani Makiyaya dauki kan kiwon Lafiya

Babban malamin addinin Islama, wanda kwararre ne fannin Kiwon lafiya da kuma tsohon soja, ya kaiwa Fulani Makiyaya tallafin kayan kiwon Lafiya a dajin jihar Kogi.

 

Kakakin Sheikh Gumi, Malam Tukur Mamu ne ya bayyana haka inda yace kwanaki kadan bayan kaddamar da makarantar fulani makiyaya a Kaduna, Sheikh Gumi ya kuma kai daukin kayan kiwon Lafiya a rugar Ardo Zubairu dake karamar hukumar Yagba a jihar Kogi.

 

Sheikh Gumi ya kaiwa Fulanin ziyarane tare da tawagarsa ta mutane 40 ciki hadda ‘yan Jarida. Fulanin wanda suka baro yankin kudu maso Gabas ne saboda yawaitar hare-haren kungiyar IPOB.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *