Wanda ya assasa Soyayya Iyali Daya (One Love Family), Satguru Maharaj ji, yayi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kama Sheikh Gumi saboda taimakawa yan bindinga da yan ta’adda.
Satguru Maharaj ji, ya bayyana hakan ne a jiya, inda ya yace maganganun da Gummi yayi a gidan talabijin wanda ya bayyana dalilin da yasa yan bindinga suke garkuwa da mutane, ya nuna cewa yana kokarin wanke su a idon duniya.
Ya kuma ce, yaji Gumi yana fada a cikin wani shiri na gidan talabijin cewa Fulani sun shiga satar mutane ne don neman kudi, tunda ba su da aikin yi, yana mai cewa irin wannan hujja ba ta da amfani kuma tana da hadari ga zaman lafiyar kasar.
Ya kara da cewa Gumi, ya kasance a kan teburin tattaunawa da shugaban kungiyar Fulani’ yan bindinga, Dogo Gide da kungiyarsa kan daliban da aka sace da mambobin Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati, Kagara a Jihar Neja, wannan sai bai kamata ba.
A karshe yace a bisa wadannan bayanai, yana rokon Gwamnatin Tarayya da ta kama Sheikh Gumi tare da hukunta shi.