fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Shirin Dadin Kowa na Arewa24 ya ci karo da Lokacin Sallah dan haka a canja masa Lokaci>>Iyaye

Wasu iyaye sun koka da cewa, shirin dadin Kowa na tashar Talabijin din Arewa24 ya ci karo da lokacin Dallah wanda hakan yake hana yara gudanar da ibada yanda ga kamata, musamman a watan Ramadana.

 

Sun bayyanawa Daily Trust cewa, shirin ya ci karo da lokacin Ibada wanda ake nunawa ranar Asabar a kuma maimaita Ranar Talata. Sunce Shirin yayi daidai kusa da lokacin sallar Isha’i da Taraweeh wanda hakan ke sanya Wasu yaran da ma manya su kwammace kallon shirin maimakon zuwa Ibada.

 

Da aka tuntubi masu kula da gidan talabijin din, sun bayyana cewa, ba zasu yi magana da manema labarai ba. Saidai wata Majiya dake kusa da gidan talabijin din ta bayyanawa gidan jaridar cewa, ba za’a iya canja lokacin nuna shirin Dadin Kowa ba saboda tasharta kasa da kasa ce.

 

Majiyar tace saboda lokutan dake sauran kasashen Duniya dake kallon tashar wanda sun banbanta, ba zata iya canja lokacin shirin ba. Ta kara da cewa idan mutum da gaske yana son yin Ibada, babu abinda zai hanashi.

“To avoid any inconveniences to the Arewa24 audiences in other countries, the timing must remain unchanged because of the time differences,” the source added. The source said no television programme would distract or divert ones attention to prayers if he or she has the intention to pray.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *