fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Shugaba Buhari na cigaba da jagorantar taron tsaro a fadar shugaban kasa

Shugaba Muhammadu Buhari na jagorantar ci gaba da taron tsaro a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Taron wanda Buhari ya kira a ranar Juma’ar da ta gabata, an dage taron ne zuwa ranar Talata.
Wadanda ke wurin taron sune Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo; Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da Shugaban Ma’aikata na Shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.
Sauran sun hada da Ministan Tsaro, Manjo-Janar Bashir Magashi (Mai ritaya) da mai ba Shugaban kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (Mai Ritaya.)
Babban hafsan tsaro, Janar Lucky Irabor, shugaban hafsoshin soja; Laftana-Janar Ibrahim Attahiru, Babban hafsan sojojin ruwa; Vice Admiral Awwal Zubairu, da Babban hafsan sojojin sama, Air Marshal Isiaka Amoo duk suna halartar muhimmin taron.
Mukaddashin Sufeto Janar na ‘yan sanda, IGP, Usman Baba shi ma ya halarci taron.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *