fbpx
Sunday, September 26
Shadow

Shugaba Buhari ya amince da biliyan N8.5 domin bincike-bincike

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kashe Naira biliyan 8.5 don gudanar da bincike mai zurfi a bangaren magunguna da sauran fannoni a shekarar 2021, a karkashin Asusun Bincike na Kasa, NRF, wanda shirin ya samu tallafin daga Asusun Ilimin Manyan Makarantu, TETFund.

Sakataren zartarwa na TETFund, Farfesa Suleiman Bogoro, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a taron karawa juna sani na kwanaki 3 ga daraktocin bincike da ci gaban jami’o’in gwamnati a Najeriya wanda aka gudanar a Babban Bankin Najeriya, CBN, Cibiyar Horarwa, Maitama, Abuja.

Shugaban TETFund ya ce asusun an shirya shi ne don sanya kudi a Cibiyar Nazarin Likitocin Najeriya, NMIR, don farfado da maganin rigakafin da suke yi.

Ya kara da cewa ya shirya ganawa da Darakta-janar na NMIR, Farfesa Babatunde Salako, tare da hazikan kwararrun malaman likitanci daga wasu jami’o’in da ke fadin kasar nan da nufin cimma wasu manufofin bincike na musamman.

Ya jaddada bukatar hada kai tsakanin jami’o’i da cibiyoyin bincike don sanin abin da cibiyoyin ke yi tare da bayar da taimako a inda ya dace.

Ya kalubalanci malaman jami’a da cewa ba wai kawai su nuna wa kansu taken ba amma su tsunduma cikin binciken magance matsaloli wanda zai sauya abubuwa don amfanin kasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *