fbpx
Sunday, September 26
Shadow

Shugaba Buhari ya amince da gina bariki ga ma’aikatan hukumar NDLEA

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da gina barikoki ga ma’aikatan hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, a fadin kasar nan.

Shugaban hukumar NDLEA, Buba Marwa, ya bayyana hakan ga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan ya yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari bayanin ayyukan hukumar a fadar shugaban kasa dake Abuja, ranar Juma’a.

Shugaban na NDLEA ya ce gina barikoki ga ma’aikatan hukumar ya zama wajibi don kare su da iyalansu daga masu aikata miyagun laifuka.

Marwa ya kara bayyana cewa ya nemi a dauki karin ma’aikata don baiwa hukumar damar gudanar da ayyukan ta cikin sauki da himma.

Dangane da ayyukan hukumar, Mista Marwa ya bayyana cewa hukumar ta kwace miyagun kwayoyi da suka kai sama da naira biliyan 100, yayin da aka ajiye kudaden da aka gano daga hannun dillalan miyagun kwayoyi a babban bankin Najeriya.

Ya kara da cewa; Tuni Hukumar ta NDLEA ta nemi izinin kotuna domin lalata magungunan da sauran kayan da ke sa maye da suka kwato.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *