fbpx
Thursday, July 29
Shadow

Shugaba Buhari ya amince da kafa cibiyar ayyukan noma a jihar Nasarawa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kafa Cibiyar Injinan Masana’antu da Inganta kayan aikin noma a jihar.

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya fadi haka ne a Lafia ranar Asabar a bikin bude Lafia City mall, reshen rukunin Kamfanonin Wave Mart.

Sule ya ce cibiyar za ta kasance ne a Lafia a matsayin ci gaba ta fuskar bunkasa masana’antu a jihar.

Ya kara da cewa hakan ya nuna a shirye jihar take ta kara fadada damammaki daban-daban a bangaren noma musamman aikin gona.

“Mun shirya a nan Lafiya. Lafia tana jan hankali sosai a fannin bunkasa masana’antu. Ina murna sosai.

“Ina so in yi amfani da wannan damar in mika matukar jinjinawa ga Shugaba Muhammadu Buhari. Bayan ‘yan makonnin da suka gabata, mun fahimci cewa kusan cibiyoyi uku ko huɗu ake shirin kafawa.

“Yanzu na rubuta don kafa cibiyar a cikin jihar kuma a jiya kawai, Shugaban ya amince da shi kuma za mu kafa wannan cibiyar a nan cikin lafia,” in ji shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *