fbpx
Monday, November 29
Shadow

Shugaba Buhari ya baiwa jami’an tsaro umarnin kara tsaurara matakai akan hanyar Kaduna zuwa Abuja

Biyo bayan yawaitar hare-haren dake faruwa a tsakanin hanyar Kaduna zuwa Abuja inda aka sace mutane da dama, shugaba Buhari ya bada umarnin kara tsaurara tsaro a hanyar.

 

Sama da matafiya 20 ne aka samu rahoton cewa an sace a hanyar cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, sannan kuma hare-haren sun yi sanadiyyar mutuwar Sagir Hamida wanda jigo ne a jam’iyyar APC ta jihar Zamfara.

 

Shugaba Buhari yace dolene a tashi tsaye wajan samar da tsaron.

 

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan taron majalisar tsaro da shugaba Buhari yayi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *