fbpx
Monday, November 29
Shadow

Shugaba Buhari ya kaddamar da kudin E-Naira

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ƙaddamar da kuɗin intanet na ƙasar e-Naira ko kuma nairar da ake kashewa ta intanet.

Shugaban ya ƙaddamar da kuɗin intanet ɗin ne ranar Litinin a Abuja, babban birnin ƙasar.

Tun farko an tsara ƙaddamar da kuɗin intanet ɗin ne a farkon wannan wata, amma sai Babban Bankin Nijeriya ya ɗage batun zuwa gaba.

Bankin ya ce ya shafe shekaru yana bincike a kan e-Naira kuma “an ɓullo da ita ne da zummar sauƙaƙa wa kowane ɓangare na al’umma gudanar da harkokin kuɗinsu”.

Tun da farko Babban Bankin Najeriya, CBN, ya ce a watan Oktoba ‘yan kasar za su soma amfani da kuɗin intanet na e-Naira.

CBN ya bayyana haka bayan ya haramta amfani da kudin Cryptocurrency saboda rashin gamsuwa da yadda tsarinsa yake.

e-Naira kudi ne da zai bai wa mutane damar yin harkokin kasuwanci ta intanet.

Tsarin zai yi aiki da kamfanin fasaha na Bitt Inc., a kokarin fara amfani da kudin intanet na e-Naira.

CBN ya zabi Bitt Inc. daga cikin manyan kamfanonin fasaha da dama da suka fafata wajen ganin sun samu kwangilar aiki tare da Bankin domin samar da wannan kudi cikin tsaro da tsari mai inganci.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *