fbpx
Thursday, July 29
Shadow

Shugaba Buhari ya nada sabbin sakatarori dindindin guda 5

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a ya sanar da nadin sabbin sakatarorin din-din-din a ma’aikatun gwamnatin tarayya.

Shugaban ma’aikatan gwamnati na tarayya (HOCSF), Dr. Folasade Yemi-Esan ne ta tabbatar da nadin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

Sakatarorin din-din-din da aka nada sun hada da Mr Adebiyi Olufunso, (Ekiti), Mrs Maryann Onwudiwe, (jihar Enugu), Mr Yusuf Ibrahim, (jihar Katsina), Mista Ogunbiyi Olaniyi, (na jihar Lagos) da kuma Mista Ibrahim Kana, na jihar Nasarawa.

Yemi-Esan ta kara da cewa za a sanar da ranar rantsar da wadanda aka nada a lokacin da ya dace.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *