fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Shugaban kasar Ghana ya buɗe babban masallacin

hugaban ƙasar Ghana Nana Akufo-Addo ya kaddamar da babban masallacin kasar a Accra babbab birnin Ghana a ranar Juma a 16 ga watan Yuli.

Masallacin wanda shi ne na biyu mafi girma a Afrika ta Yamma yana da Ofishin babban limamin kasa da asibiti da dakunan gwaji da wurin sayar da magani da dakin karatu da kuma wajen ajiye gawa.

Cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook shugaban ya ce buɗe masallacin ya samu halartar manyan baki ciki har da wasu shugabanni daga kasashen ketare.

Shugaban ya wallafa hotunan bude masallacin akalla sun kai 40.

Bayan nan kuma shi da wasu jagororin kasar sun nuna girmamawarsu ga shugaban Nijar da ya bar gado Mahamadou Issoufou, wanda Shugaba Nana ya bayyana a matsayin “Aboki kuma dan uwa” wanda ya jagoranci tabbatar da kungiyar kasuwanci kasashen Afrika mara shinge.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *