fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Shugaban Majalisar Dattawa ya ba da gudummawar Naira miliyan 8 ga wadanda iftila’in gobara ya shafa a kasuwar Yobe

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya bayar da gudummawar Naira miliyan 8 ga wadanda iftila’in gobarar kasuwar ‘Yan Harawa ya shafa a Jihar Yobe.

A cikin wata sanarwa da Ezrel Tabiowo, mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai na Sanata Lawan ya fitar, yace an bayar da gudummawar ne a lokacin da ya kai ziyara kasuwar Gashua, karamar hukumar Bade ta jihar Yobe.

Lawan ya yi kira ga shugabannin kungiyar kasuwar Yan Harawa da su tabbatar da cewa duk wadanda iftila’in gobara ya shafa sun amfana daidai da gudummawar ba tare da la’akari da bangaren jam’iyya ko addini ba.

Lawan ya bayar da tabbacin cewa Gwamnatin Tarayya ta hanyar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) za ta kuma tallafa wa wadanda gobarar ta shafa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *