fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Shugaban Masu addinin gargajiya da suka kashe Musulmi a cikin masallaci da aka kama, yace bashi da lafiya, ba zai iya tsayawa a yi shari’a ba

Shugaban masu addinin gargajiya da aka kama a jihar Osun saboda kai hari kan masallaci da kashe masallaci, Kayode Esuleke ya bayyana cewa bashi da lafiya ba zai iya tsayawa a yi mai shari’a ba.

 

Lauyansa, Kehinde Abioye ne ya bayyana haka a ranar Lahadi. Yace yana Asibiti ana bashi kulawa.

 

An dai kama shugaban addinin gargajiyan da shugaban masallacin Kamaruddeen da lamarin ya faru.

 

Masu addinin gargajiyan sun zargi mutanen masallacin ne suka tsokanesu fada. Rahoton yace, da zarar Shugaban masu addinin gargajiyanya samu sauki, za’a ci gaba da shari’a.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *