fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Shugabannin PDP sun roki Jonathan kar ya fice daga jam’iyyar

Shugabannin babbar jam’iyyar adawa ta PDP sun ziyarci tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan domin rokonsa ya ci gaba da zama a jam’iyyar.

Mukadashin shugaban jam’iyyar, Yemi Akinwonmi ne ya jagoranci tawagar da ta ziyarci Jonathan a gidansa da ke Abuja.

Duk da cewa tawagar ta yi ganawa da tsohon shugaban a cikin sirri, wasu rahotanni na cewa sun tattauna kan rigingimun cikin gidan jam’iyyar da kuma neman shawarwari kan yada za a lalubo bakin zaren.

Sannan wata majiya na cewa tawagar ta nemi alfarma wajen Jonathan kan kada ya fice daga jam’iyyar, sannan ta nemi ya kasance tare da su da shigar da kansa lamuran jam’iyyar domin ganin sun kai ga nasara.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *