fbpx
Sunday, September 26
Shadow

Shugabar NPA, Hadiza Bala Usman ta ba da tallafin kayan agaji ga ‘yan gudun hijira a Katsina

Manajan Daraktan Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA), Hajiya Hadiza Bala Usman ta ba da kayan agaji ga wadanda aka yi garkuwa da su a karamar hukumar Matazu, jihar Katsina.

Yayin da ta ke mika kayan ga wadanda abin ya shafa, Hajiya Jamila Abdu Mani a madadin maigidan NPA ta yi kira ga masu hannu da shuni da su yi koyi da irin wannan taimakon ta hanyar ba da karin kayan ga marasa karfi.

Ta ce gudummawar wani bangare ne na kokarin rage radadin wahalar da wadanda abin ya shafa ke fuskanta.

Abubuwan da aka bayar sun haɗa da Buhunan shinkafa, jaruman mai, katon-katon na gishiri, sabulun wanka dana wanki, kondunan shara, da sauransu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *